(ABNA24.com) Gwamnatin kasar Rasha ta rubuta wasiku guda biyu ga majalisar dinkin duniya dangane da tabbatar da tsaro a yankin tekun farisa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wasikun biyu, sun isa komitin tsaro na majalisar dinkin duniya da kuma babban zauren majalisar.
Banda haka kamfanin dillancin labarai na TASS na kasar Rasha, ya ce ya sami kofin wasikun biyu a yau Talata a birnin Mocso.
A cikin shawarar da gwamnatin kasar Rasha ta gabatar a cikin wasikun dai, akwai bukatar tattaunawa tsakanin kasashen yankin tekun farisa a tsakaninsu, sannan komitin tsaro na majalisar dinkin duniya, da kungiyar kasashenn laraba, da kungiyar kasashen musulmi, da kuma kungiyar kasashen larabawa na yankin tekun farisa, ya zama suna da wakilan a tattaunawar.
Gwamnatin Rasha ta kammala da cewa a shirye take ta bada hadin kai ga dukkan bangarorin da abin ya shafa don tabbatar da zaman lafiya da nutsuwa a yankin tekun farisa.
/129
31 Yuli 2019 - 04:06
Lambar labari: 965915
Gwamnatin kasar Rasha ta rubuta wasiku guda biyu ga majalisar dinkin duniya dangane da tabbatar da tsaro a yankin tekun farisa.